×
  • News - North East - Taraba
  • Updated: July 08, 2021

Gwamna Yayi Kira ga Gwamnatin Tarayya da Ta Maida NYSC Shekaru Biyu

Gwamna Yayi Kira ga Gwamnatin Tarayya da Ta Maida NYSC Sheka

Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, ya bayyana cewa ya kamata Gomnatin Tarayya ta ba wa masu bautar kasa (NYSC) horo na soja domin sanin yadda ake sarrafa bindigogi don kare kan su.

Gwamnan ya kuma ce kamata ya yi a tsawaita tsawon lokacin shirin daga shekara daya zuwa shekara biyu domin bayar da isashshen horo ga wadanda suka kammala karatun.

Ya bayyana hakan ne a daren Laraba lokacin da ake hira da shi a cikin shirin ’Politics Today' na gidan talabijin din Channels.

Ishaku, wanda jiharsa tana daya daga cikin jihohin Arewa maso Gabas da rikicin Boko Haram ya shafa hade da kashe-kashen da mayaka masu dauke da makamai suka yi, ya jaddada cewa ya kamata a ba ‘yan kasa damar daukar makamai su kare kansu daga masu yi musu ta’adi.

Gwamnan bayyana cewa, “Lokacin da jami'an tsaro ba za su iya kare ku ba, to dole ne a samu madadin hakan, dole ne mu kasance masu aiwatarwa. A koyar da mutane, a basu dama, a barsu su san abin da za su yi.

“NYSC da zan ce, ya kamata ya zama shekara biyu. Shekara daya don horon soja na tilas, da kuma wata shekara ta ayyukan zamantakewar da suke yi a yanzu domin duk wanda ya kammala aikin NYSC zai iya sanin yadda zai rike bindiga, ya kare kansa kamar yadda ake yi a Isra’ila, Lebanon da sauran wurare , dole ne ka jawo hankalin 'yan kasar ka su zama masu himma.

"Lokacin da ba za ku iya samar da tsaro ba, dole ne ku bar mutane su kare kansu."

Ya koka kan yadda 'yan ta'adda da' yan dadi bindiga ke addabar mutane, suke yin barna ba tare da tsammani ba, da zubar da jini a yankin Arewa maso Gabas wanda kuma wasu masu fada a ji ke daukar nauyin su.

“Akwai masu daukar nauyinsu, wadannan sababbin samfurin AK-47 ne. Ta yaya mutumin kauye zai sayi irin wannan makamin mai tsada? A cikin faifan bidiyo ne kuma ya yadu wani ya furta cewa ana basu bindigogin kuma ana basu horo kan yadda ake amfani da su. Aikin jami'an tsaro ne don gano asalin wannan.

"Idan za su iya fita daga kasar nan su kamo wani da yake ikirarin samun 'yanci, me ya sa ba zai yiwu ba su kare mutanenmu da ake kashewa a gonaki?" Ishaku ya tambaya.

Ishaku ya nuna kwarin gwiwa cewa za a iya shawo kan rashin tsaro a yankin da kuma duk sassan kasar lokacin da masu fada aji na siyasa da jami'an tsaro suka hura wuta don tabbatarwa a shirye suke su kawo karshen matsalar.

Related Topics

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Comment(s)

See this post in...

Notice

We have selected third parties to use cookies for technical purposes as specified in the Cookie Policy. Use the “Accept All” button to consent or “Customize” button to set your cookie tracking settings