×
  • News - North East - Taraba
  • Updated: July 07, 2021

Gwamnonin Arewa Maso Gabas sun Tattauna kan Kalubalen Yankin da Yunkurin Magance Su

Gwamnonin Arewa Maso Gabas sun Tattauna kan Kalubalen Yankin

Abdulrazak Muhammad

A ranar Talata ne Gwamnonin Arewa maso Gabas sukayi taro karo na biyar a garin Jalingo dake Jihar Taraba.

Taron wanda ya samu halartar gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe sun tattauna akan matsalolin da ke addabar yankin.

A wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Farfesa Babagana Umara Zulum FNSE, Mni, gwamnan jihar Borno, tattaunawar da gwamnonin sukayi,  sun lura da ci gaban da aka samu a fanin tsaro na yankin.

Gwamnonin sun yaba wa hukumomin tsaron Najeriya tare da yin kira da a ci gaba da hadin kai tsakanin su.

Baya ga haka, sun kara kira ga ƙungiyoyin diflomasiyya, abokan haɗin gwiwa da hukumomin bayar da tallafi waɗanda ke tallafawa yankin da su dau damaran  "yin ƙaura daga ayyukan jin kai zuwa tabbatar da zaman lafia Mai daurewa a cikin yankin."

Yayin da gwamnonin suka lura da mummunan tasirin kwayoyi da kayan maye a yankin sukeyi, kungiyar ta yi kira da a tallafa don dakile matsalar a cikin garuruwa da kan iyakokin su.

Kungiyar ta shirya zama na gaba ne a ranar Asabar, 9 ga Oktoba 2021, a Damaturu, Jihar Yobe.

Related Topics

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Comment(s)

See this post in...

Notice

We have selected third parties to use cookies for technical purposes as specified in the Cookie Policy. Use the “Accept All” button to consent or “Customize” button to set your cookie tracking settings