×
  • News - North East - Taraba
  • Updated: July 07, 2021

Gwamnonin Arewa Maso Gabas Sunyi Kiran Hadin Gwiwa da NEDC 

Gwamnonin Arewa Maso Gabas Sunyi Kiran Hadin Gwiwa da NEDC 

Abdulrazak Muhammad

Kungiyar gwamnonin arewa maso gabas karkashin jagorancin gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum tayi kiran hadin gwiwa da hukumar ci gaban yankin arewa maso gabas (NEDC).

Yayin da aka damu da rashin tuntuba tsakanin gwamnonin jihohin yankin da NEDC akan zaben inda ya cancanta ayi aiyuka, kungiyar ta bayyana cewa ayyukan da suke gudana a Yankin na tafiyar hawainiya.

Kungiyar ta yi kira ga hadin gwiwa, inda ta bukaci gwamnonin da su zaba wuraren ayyukan kamar yadda aka tsara ci gaban yankin Arewa maso Gabas.

Taron ya kuma yi kira ga Arewa Research and Development Project (ARDP) da ta gabatar da tsare-tsaren ta ga Sakatariyar kungiyar gwamnonin "don ci gaba da yada shi zuwa Jihohi daban-daban don aiwatarwa."

Kungiyar ta ce hakan ya faru ne bisa 'lura da irin cigaban da aka samu sakamakon amfani da sabon tsarin kudi' na ARDP a jihar Adamawa.

gwamnonin sun kuma nuna rashin jin dadin su game da rashin kula na Gwamnatin Tarayya kan aikin wuta na Mambilla Hydroelectric Power Project.

Gwamnonin sunyi kira ga shugaban kasa Muhammdu Buhari "da ya baiwa aikin muhimmancin da ake bukata ta hanyar kafa Special Purpose Vehicle (SPV) don magance matsalolin da kuma kammala aikin."

A yunkurin gwamnonin na kawo gyara akan matsalolin da suka shafi fannin Ilimi a yankin, "Kungiyar ta samu rahoto daga Majalisar Ilimi na Arewa Maso Gabas kan Ilimi. Ta dauki shawarwarin majalisar akan inganta Ilimi da Kara kwazon dalibai da malamai. Kana da horas da malamai a yankin, "in ji sanarwar da kungiyar ya fitar.

Related Topics

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Comment(s)

See this post in...

Notice

We have selected third parties to use cookies for technical purposes as specified in the Cookie Policy. Use the “Accept All” button to consent or “Customize” button to set your cookie tracking settings