×
  • News - North West - Kaduna
  • Updated: July 08, 2021

Kaduna: INEC ta fitar da ranar da za a gudanar da zaben mayegurbi a Lere

Kaduna: INEC ta fitar da ranar da za a gudanar da zaben maye

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Qasa (INEC) ta sanya ranar Asabar 14 ga watan Agusta, shekarar 2021 don zaben maye gurbin mazabar Lere a Jihar Kaduna.

Kwamishina na kasa kuma shugaban kwamitin yada bayanai da ilimantar da masu zabe, Festus Okoye Esq. ya sanar wa manema labarai ta wata takarda a ranar Alhamis.

Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, Shugaban majalisar wakilai ne ya sanar da hukumar zaben rashin Mai mukamin a mazabar ta Lere.

Wannan ya biyo bayan rasuwar memba mai ci, Hon. Suleiman Aliyu Lere a ranar 6 ga watan Afrilu, 2021.

Hukumar ta kuma bayyana cewa, "Za a gudanar da zaben ne bisa la'akari da rajistar masu jefa kuri'a, da kuma wuraren da aka jefa kuri'un a babban zaben na 2019, a duk fadin mazabar da ke karkashin karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna."

Sanarwar ta kuma bayyana cikakkun bayanai game da mika fom.

Sanarwar ta bayyana cewa, "Za a buga sanarwar a hukumance game da zaben a ranar 12 ga watan Yulin 2021. Jam'iyyun siyasa za su gudanar da zaben fidda gwani tsakanin 13 zuwa 24 ga watan Yuli 2021. Hanyar samun damar shigar da fom din takara ta yanar gizo za zata fara daga 24 ga watan Yuli 2021 a hedkwatar Hukumar a Abuja. Sannan ranar karshe da za a gabatar da jerin sunayen ‘yan takarar da aka zaba shi ne 27 ga watan Yulin 2021 da karfe 6.00 na yamma.

“Jam’iyyun siyasa za su gabatar da sunayen wakilansu na Zabe don zaben ga Jami’in Zabe na INEC na Karamar Hukumar Lere a ranar ko kafin 31 ga watan Yulin 2021, kuma kamfen din jam’iyyun siyasa zai kare a ranar 12 ga watan Agusta 2021."

An daura cikakken Jadawalin ayyukan zaben maye gurbin a kan shafin yanar gizo-gizo na Hukumar da shafukan sada zumunta.

Hukumar ta kuma bukaci jam’iyyun siyasa da su bi tsarin jadawalin sannan su gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyya kamar yadda doka ta tanada.

Related Topics

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Comment(s)

See this post in...

Notice

We have selected third parties to use cookies for technical purposes as specified in the Cookie Policy. Use the “Accept All” button to consent or “Customize” button to set your cookie tracking settings